Firaministan Li ya bayyana cewa, raya tattalin arziki cikin dogon lokaci, da kyautata zaman rayuwar al'umma, da sa kaimi ga samar da daidaito a zamantakewar al'umma sun zama manyan ayyuka a gaban gwamnati mai ci yanzu. Don haka, dole ne a dauki manufar tattalin arziki daga manyan fannoni. Yanzu, lokaci ya yi da a canja salon raya tattalin arziki, ya kamata a kyautata batun raya tattalin arziki cikin dogon lokaci, a kokarin raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma gaba daya.
Li Keqiang ya ce, yanzu ba a raya tattalin arziki cikin daidaito a tsakanin birane da yankunan karkara da kuma tsakanin yankuna daban daban, sabo da haka, akwai sauran rina a kaba wajen raya tattalin arziki na yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin. Kamata ya yi a mai da hankali wajen raya muhimman ababen more rayuwa a yankunan yammacin kasar, da kuma karfafa zukatan kwararru da su yi zama a wurin.
Haka kuma, firaministan Li ya kara da cewa, yayin da ake raya yankunan yammacin kasar, dole ne a ba da tabbaci wajen kyautata zaman rayuwar al'umma, da inganta hadin gwiwa tsakanin mutane na kabilu daban daban don su samu ci gaba da wadata tare.(Bako)