Firimiyan kasar Sin Li Keqiang ya gana da firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn a birnin Beijing na kasar Sin a ranar Alhamis 13 ga wata, sun kuma tattauna kan yadda kasashen biyu za su inganta hadin gwiwa tsakaninsu. Yayin ganawar shugabannin biyu, Li ya zayyana irin kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Habasha, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakaninsu a shekarar 1970.
Ya kuma jaddada cewa, bangarorin biyu, na daukar matakan da suka dace, domin inganta tattalin arziki, da rayuwar al'ummominsu, don haka akwai makoma mai haske ga batun hadin gwiwa tsakaninsu.
Har ila yau, Li ya kara da cewa, kasar Sin na ci gaba da baiwa dukkanin kamfanoni da suke da kwarewa tallafi, wajen aiwatar da ayyukan samar da ababen more rayuwa, da makamashi, da kafa masana'antu, kere-kere da kuma harkar noma a kasar ta Habasha, yana mai kira ga shuwagabannin kasashen Afirka, da su kafa tsare-tsare, da za su ba da damar yin hadin gwiwa a fannonin al'adu, da ilimi, da yawon shakatawa, tare da share fagen tattauna batutuwan da suka shafi kasa da kasa, ciki hadda batun gyaran fuska ga kudurorin kwamitin tsaron MDD, don gane da rikicin dake addabar kasashen Somaliya, da na tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.
A nasa jawabi, firaministan kasar ta Habasha Hailemariam Desalegn, zayyana irin kokarin da kasarsa ke yi ya yi, musamman a fagen bunkasa dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, yana mai maraba da dukkanin kamfanonin kasar dake fatan zuba jari a Habasha. Desalegn ya jinjinawa irin rawar da kasar Sin ke takawa, a fannin bunkasa ci gaban nahiyar Afirka. (Saminu)