Li Keqiang ya kuma kara da cewa, ya kamata a mai da hankali kan halin da muke ciki yanzu da makomar tattalin arzikin kasa da kuma tabbatar da zaman karko na manufofin kara karfin tattalin arzikin kasa.
Kan fannin manufofin kasa game da harkokin kudi, bai kamata a kara haifar da gibin kudi ba, ya kamata a aiwatar da gyare-gyare kan tsarin samar da kasafin kudi a kasa, rage yawan kasafin kudin tafiyar da harkokin mulki, da kuma gaggauta gudanar da ayyukan yin gyare-gyare da ba da tabbaci ga zaman rayuwar al'ummar kasa, musamman ma a yankunan tsakiya da kuma yammacin kasar, bugu da kari, za a ba da gatanci kan kudin haraji ga kananan kamfanoni.
Mr. Li ya bayyana cewa, an karfafa ayyukan sa ido kan kasuwar kudi don magance da kuma warware matsalolin sha'anin kudi da kila za a gamu da su a nan gaba. (Maryam)