Gwamnatin kasar Sin ta yi biki a nan birnin Beijing a ranar Litinin 30 ga wata domin murnar cika shekaru 64 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.
Bikin wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping, firaministan kasar Li Keqiang, tare da sauran manyan kusoshin kasar, da jama'ar sassa daban daban na kasar, da baki 'yan kasashen waje, baki daya mutane fiye da 1100 suka hallara.
A wajen bikin, mista Li Keqiang, firaministan kasar Sin a jawabinsa ya ce, a halin yanzu kasar Sin na cikin wani yanayi mai muhimmanci inda take kokarin sauya tsarin tattalin arzikinta, don haka ana bukatar hadin kan dukkan al'ummomin kasar don yin kokari tare. Haka zalika kuma neman samun ci gaba ya kasance aiki mafi muhimmanci na yanzu, sa'an nan kamata ya yi a tabbatar da ganin ci gaban ya samar wa jama'ar kasar da alfanu, domin a cewarsa adalcin da ake samu cikin wata al'umma shi ne tushen samun ci gabanta.
Haka zalika, yayin da ya tabo maganar huldar dake tsakanin Sin da sauran kasashe na duniya, mista Li ya ce, kasar za ta tsaya kai da fata kan turbar ci gaba irin na zaman lafiya, sa'an nan za ta nace ga manufar amfanawa juna yayin da take hadin gwiwa da sauran kasashe. Kasar Sin, a cewar firaministan, na son raba damar samun ci gaba, da zama kafada da kafada da sauran kasashen wajen tinkarar kalubale, da kokarin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar da kasar ke ciki gami da a duk duniya baki daya, don tabbatar da makoma mai haske na dan Adam.(Bello Wang)