in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
John Kerry ya yi kira da a shirya taron shimfida zaman lafiya a kasar Sham tun da wuri
2013-10-15 09:53:37 cri

Sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Kerry ya gana da manzon musamman na MDD da tarayyan kasashen Larabawa kan batun Sham Lakhdar Brahimi a ran 14 ga wata a birnin London na kasar Britaniya, inda John Kerry ya yi kira da a shirya taron shimfida zaman lafiya a kasar Sham cikin lokaci. 

Bayan ganawarsu, Kerry ya gaya wa manema labaru cewa, a ganinsa, wajibi ne a shirya taron Geneva karo na biyu a tsakiyar watan gobe. Ya ci gaba da cewa, shi da Brahimi dukkansu suna ganin cewa, abun gaggawa ne a tabbatar da lokacin taron, a kokarin samar da sabon yanayi a kasar ta Sham. A ganin Kerry, dole ne a kafa gwamnatin wucin gadi a Sham, wadda za ta tafiyar da harkokin kasar, don samun damar shimfida zaman lafiya a kasar. Shi ma a nasa bangare, Mr. Brahimi ya yi bayani cewa, a wannan mako da muke ciki, zai kai ziyara a gabas ta tsakiya, inda zai yi kokarin yin shawarwari da wakilai daga bangarori daban daban, don saurarar ra'ayoyinsu, da kuma tattaunawa da su kan lokacin da za a shirya taron.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China