Duk da haka, Obama ya kara da cewa, ba a tsara jadawalin daukar matakin soja kan Sham ba. Kasarsa za ta zabi lokacin daukar matakin da kanta. Zai nemi samun iznin majalisar dokokin kasar na daukar matakin soja. Tuni ya riga ya buga wa shugaban majalisar dokokin kasar waya, majalisar dokokin kasar za ta yi muhawara da jefa kuri'a kan lamarin cikin hanzari nan da ranar 9 ga watan Satumba.
Ban da wannan kuma, a wannan rana, Obama ya yi hira da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande ta wayar tarho a wani tsawon lokaci na fiye da mintoci 40, inda suka sake nanata aniyarsu ta yanke hukunci mai tsanani kan gwamnatin Sham. Wannan shi ne karo na 3 da shugabannin Amurka da Faransa suka tattauna batun Sham ta wayar tarho a cikin mako guda da ya gabata.
A wannan rana kuma, Martin Nesirky, kakakin magatakardan MDD ya bayyana cewa, a ranar nan, tare da abubuwan sheda da aka tattara a kasar ta Sham, kungiyar bincike ta MDD ta isa birnin Hague na kasar Holland, inda aka kafa babban zauren hukumar hana amfani da makamai masu guba. Za a yi kwanaki 2 ana bincike kan abubuwan shedan, daga baya za a mika su ga wasu dakunan gwaje-gwajen da ke kasashen Turai don su yi bincike. Mista Nesirky ya kara da cewa, kungiyar binciken za ta yi iyakacin kokarinta na gaggauta yin bincike kan abubuwan samfur din. Da zarar kungiyar binciken ta samu sakamakon bincike, za ta mika wa Ban Ki-moon, magatakardan MDD rahoto cikin hanzari game da binciken da ta yi a kasar Sham, sa'an nan mista Ban zai sanar wa kwamitin sulhu da dukkan mambobin MDD sakamakon binciken.
Har wa yau kuma, a ranar 31 ga watan Agusta, Abdullah Ensour, firaministan kasar Jordan ya jaddada a yayin wani taron da aka yi a fadar firaministan kasar cewa, ba ruwan Jordan da rikicin Sham, ta haka Jordan ba za ta zama wani dandali na daukar matakin soja kan Sham ba. Kana Mohammad-Ali Jafari, kwamandan rundunar tsaron juyin juya hali na Islama ta kasar Iran ya ce, Amurka ba za ta iya daukar nauyin mummunan sakamakon da za a samu bisa daukar matakin soja kan Sham ba.(Tasallah)