A kasar Sham, fashewa mai karfin gaske da ake tabbatar da cewar daga wani bam ne da aka dana cikin wata mota ta shafi harabar filin saukar jiragen saman sojoji a al-Mazzeh, dake yammacin babban birnin kasar, kamar yadda wassu masu fafutuka da kafofin yada labarai suka tabbatar.
Gidan talabijin mai goyon bayan gwamnatin kasar 'Sama TV' ta sanar da cewar, maharan sun so su kai harin ne ga sansanin sojin na al-Mazzeh daga nan kuma ba ta yi wani karin bayani ba.
Sai dai kuma kungiyar kula da kare 'yancin al'umma na kasar Sham dake zaune a kasar Ingila ta ce, fashewar ta auku a cikin wata mota da aka dana ta dab da wani wurin bincike motocin masu wucewa dake dab da filin saukar jiragen saman.
Wata kungiyar fafutuka kuma, mai suna kwamitin tsare-tsare na cikin gida ta ce, wuta ce ta tashi a wajen filin saukar jiragen saman sakamakon fashewar wannan bam din, sai dai wannan bayanin ba a iya tantance shi ba dalilin rashin rahoton manema labarai a hukumance.
Filin saukar jiragen saman dai yana kusa da Daraya da Muadamieh inda ake gwabza fada tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan adawan da kasashen yammaci ke mara ma baya.
Su dai 'yan adawan suna zargin cewa, daga sansanin saukan jiragen saman ne ake harba yawancin makamai a kan Daraya da Muadamieh. (Fatimah)