in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya ce za a yi kokarin hade tattalin arzikin kasar Sin da na kasar Amurka
2013-06-06 20:46:14 cri
A ranar Laraba 5 ga wata a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da Henry M. Paulson, tsohon sakataren kudin kasar Amurka, inda Li Keqiang ya ce, kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Amurka a fannoni daban daban, ta yadda za a iya kara hade tattalin arzikin kasashen biyu, kafa yanayin yin takara cikin adalci da moriyar juna da kuma samun nasara tare tsakanin masana'antunsu.

Li Keqiang ya kara da cewa, kasashen Sin da Amurka na kokarin kafa sabuwar hulda tsakanin manyan kasashen biyu. Shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama nan da jimawa kadan, sabo da haka, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu wata sabuwar damar neman ci gaba.

Sannan Li Keqiang ya bayyana wa bako nasa yadda gwamnatin kasar Sin ke kokarin yin gyare-gyare kan hukumomin dake karkashinta.

A nasa bangare kuma, Henry M. Paulson ya bayyana cewa, al'ummar kasar Amurka na mai da hankali sosai kan yadda kasar Sin ke yin gyare-gyare da canja nauyin da ake dorawa hukumomin gwamnatin kasar Sin, sabo da wannan zai taka rawa sosai wajen ciyar da kasar Sin gaba, kuma zai samar da sabuwar dama ga kokarin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Amurka da Sin. Masana'antu da 'yan kasauwa na kasar Amurka suna fatan kasashen biyu za su samu nasarar yin shawarwarin daddale yarjejeniyar kare zuba jari tsakanin Amurka da Sin, kuma suna fatan za su iya taka rawa kan wannan shawarwari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China