Manyan jami'an zartaswa da shugabanni na kamfanonin kasa da kasa sama da goma wadanda suka zo kasar Sin don halartar taron tattaunawar batun arziki da taron kwamitin manyan jami'an zartaswa na kasa da kasa sun halarci shawarwarin.
Li Keqiang ya gabatar wa baki halin tattalin arziki da ake ciki a kasar Sin, kuma ya karfafa zukatan wadannan manyan 'yan kasuwa da su yi amfani da babbar dama da aka samu a kasar Sin, don karfafa hadin gwiwa da kasar Sin.
Wakilan 'yan kasuwa sun bayyana cewa, sun yi musayar ra'ayi a tsakaninsu game da babbar damar da aka samu a kasar Sin, da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci, da kirkiro sabbin fasahohi da canja salon raya tattalin arziki, da batun mai da kasar Sin ta zama mai kunshe da alkaryu da garuruwa na zamani, da raya makamashi, kuma a cewarsu, suna dora muhimmanci sosai game da kasuwannin kasar Sin da makomar raya kasar .(Bako)