in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa, Amurka da kuma Birtaniya sun cimma matsaya kan batun makamai masu guba na Syria
2013-09-18 21:57:35 cri
A ranar Litinin 16 ga wata, bayan da ya yi shawarwari da sakataren harkokin waje na Amurka, John Kerry da ministan harkokin waje na Birtaniya, William Hague, shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana cewa, kasashen uku sun riga sun cimma matsaya a kan daftarin da za su baiwa kwamitin sulhu na MDD dangane da makamai masu guba na Syria.

Fadar shugaban Faransa ta ba da labarin cewa, wannan daftari na da karfi sosai, kuma ya kunshi hakikanin wa'adin lalata makaman na Syria.

A cikin shawarwarin, shugaba Hollande ya jaddada cewa, Faransa da Amurka da kuma Birtaniya za su dauki ra'ayinsu mai karfi, da fatan za a sa kaimi ga kwamitin sulhu na MDD domin zartas da kuduri kan wannan batu cikin makon da ake ciki. Rahoton da masu bincike na MDD za su bayar zai taimaka wajen zartas da kudurin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China