in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar EU da ta UNICEF zasu taimakawa jihar kano dake arewacin Najeriya wajen gina fanfunan tuka-tuka 500
2013-09-10 15:40:06 cri

Kananan hukumomi biyu ne zasu fara amfana da kashin farko na aikin gina rijiyoyin tuka-tuka, da kungiyar tarayyar turai EU da kuma ta UNICEF zasu samar bisa hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano.

Manajan daraktan hukumar samar da ruwan sha a yankunan karkara ta jihar Kano (RUWASA) Injiniya Abdullahi Idris Karaye ne ya tabbatar da hakan, lokacin da ya ke ganawa da wakilin gidan rediyon CRI a kano.

Injiniya Abdullahi Idris yace daman wadannan kungiyoyi tuni suka nuna sha`awarsu ta bayar da tallafinsu, wajen warware matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha a yankunan karkarar dake jihar Kano, amma wasu matsaloli da suka fuskanta a gwamnatin data shude suka dakatar da shirinsu.

Yace yanzu sakamakon ganin irin himmar da gwamnanti mai ci ke nunawa kan sha`anin ruwan sha ya sanya yanzu hankulansu ya dawo jihar Kano, inda suka ci alwashin narkar da kudade masu tarin yawa domin cimma wannan buri nasu .

To ko akwai wani tallafin kudi daga bangaren gwamnati wajen gudanar da wannan aiki? Injiniya Abdullahi Idris Karaye ya ce kwarai akwai tallafin gwamnatin jihar Kano, kan wannan aiki da wadannan hukumomin za su gudanar.

A wasu lokutan dai irin wannan aiki yana daukar lokaci mai tsawo kafin a fara shi, akan haka ne na tambayi shugaban hukumar ta RUWASA wa`adin da aka diba domin fara aikin?

Manajan daraktan hukumar ya tabbatar da cewa nan da watan gobe za a fara aikin gina rijiyoyin, kasancewar yanzu hadin gwiwar injiniyoyin hukumar da na kungiyoyin EU da UNICEP suna aikin nazari kan yadda za a tsara aikin.

Daga karshe Injinya Abdullahi Idris ya baiwa dukkan masu sha`awar saka jari, da `yan kasashen waje tabbacin samun hadin kan gwamnatin Kano a ko da yaushe.

A `yan shekarun baya al`ummomi mazauna karkara a jihar Kano sun sha fama da cututtukan da suke da nasaba da rashin tsaftaccen ruwa sha, lamarin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dama a wancan lokaci.(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China