Dr. Anuforom yayi wannan furuci ne a wajen wani taron manema labarai da aka yi a ranar Alhamis a birnin Abuja, inda ya jaddada cewa, hukumarsa ta kara samun kwarewa wajen yin hasashen yanayi yadda ya kamata.
Dr Anuforom ya ce jihohin hudu, da suka hada da Bauchi, Gombe, Filato da kuma Kaduna suna fama da ruwan sama sosai a wadannan kwanaki, kuma idan aka ci gaba da yin ruwan sama kamar da bakin kwarya, za'a fuskanci ambaliyar ruwa a wadannan wurare.
Babban darektan ya kara da cewa, hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta samu amincewa daga kungiyar tabbatar da mizani ta kasa da kasa wajen samar da hidimomin hasashen yanayi a manyan filayen saukar jiragen sama hudu dake kasar, ciki har da Abuja, Lagos, Kano da Patakwal.
Yayi bayanin cewa a sakamakon sabuwar fasahar da hukumarsa ke amfani da ita, zata iya yin hasashen yanayi daga kwanaki uku zuwa goma kafin abkuwar lamarin. (Murtala)