'Yan kungiyar sun yi arangama ne da jami'an tsaro na Sojoji da sanyin safiyar yau din abin da ya zame na farko da hakan ya taba faruwa tun lokacin da kungiyar ta fara barazana ga zaman lafiyar al'umma a 2009,kamar yadda wata sanarwa daga ofishin tsaro ta sanar.
A lokacin wannan arangama da aka yi musayar harbe harbe wasu mutane sun samu rauni sannan an kama 'ya 'yan kungiyar da ake zargi da kai wannan hari da yawansu.(Fatimah Jibril)