A cikin wata sanarwar da kakakin Jam'iyyar Lai Mohammed ya saka ma hannu aka kuma fitar ma manema labarai a birnin Ikko,jam'iyyar ta kira wannan kisa aikin rashin tausayi da imani kuma abin da baya da hujjar aikata shi.
A kalla dalibai 40 suka mutu a kwalejin koyon aikin gona lokacin da 'yan kungiyar nan ta boko haram suka kai masu hari cikin dare.
Jam'iyyar ta yi kira da a dakatar da kai irin wadannan hare hare a dawo teburin tattaunawa domin a samun zaman lafiya da tsaro a kasar baki daya.
Dakatar da bude wuta abu ne da ya kamata a yi shi ba tare da wani bata lokaci ba in ji Lai Mohammed,tare da kira ga sarakunan gargajiya,da shugabannin addini,siyasa da sauran masu fada a ji a wauraren da wadannan fitinu suka yi kamari da su tsoma baki don ganin an samu masalaha tare da kawo karshen wannan tashin hankali da kungiyar ke jefa al'umma a ciki.(Fatimah Jibril)