Gwamnan Jihar Alhaji Umaru Tanko Al-Makura wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai yace fadan bayan asarar rayuka da gidaje sama da 1,300 da ya janyo ya kuma kawo rashin kwanciyar hankali a tsakanin al'ummomin Eggon da Alago.
Fadan dai ya barke ne a ranar juma'ar data gabata har kashegarin asabar inda ya shafi yankunan Assakio dake karamar hukumar lafiya da kuma babban garin karamar hukumar Obi.(Fatimah Jibril)