Mai bada shawara kan kafofin watsa labaru na fadar shugaban kasar Nijeriya, mista Reuben Abati ya ba da wata sanarwa inda ya nuna cewa, shugaba Goodluck Jonathan ya nuna fatan cewa firaminista Tony Abbot zai ci gaba da yin kokari tare da kawancen jam'iyyar adawa da ke karkashin jagorancinsa don inganta dangantakar zumunci da ke tsakanin kasarsa da Nijeriya, har ma tare da kasashen Afirka baki daya. Ya kuma nuna cewa, shugaba Jonathan da kuma gwamnatin Nijeriya suna cigaba da hadin gwiwa tare da firaminista Abbot da gwamnatin kasarsa wajen karfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayyar tsakanin kasashen biyu.
Sanarwar ta bayyana cewa, shugaba Jonathan ya yi imanin cewa, a karkashin jagorancin gwamnatin firaminista Abbot, kasashen Nijeriya da Australia za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa da cudanyar juna kan harkokin kasa da kasa, da suka hada da yaki da 'yan ta'adda, canjin yanayi da kuma bunkasa cinikayyar kasa da kasa da dai sauransu. (Maryam)