in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin ruwa da ya nutse a Nijeriya ya haddasa mutuwar mutane a kalla 42.
2013-09-29 10:49:07 cri
Rahotanni daga tarayyar Nijeriya sun tabbatar da aukuwar wani hadarin jirgin ruwa a birnin Minna na jihar Niger, wadda ke yankin tsakiyar kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 42, baya ga wasu mutane kimanin 100 da har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger Ibrahim Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa jirgin ruwan da ke dauke da fasinja kimanin 150, ya nutse ne a wani wuri da ke kusa da garin Malale daura da kogin Kwara. Ya ce akasarin fasinjojin da ke jirgin 'yan kasuwa ne dake zuwa cinikayya kauyukan dake makwaftaka da su.

Hussaini ya ce, ya zuwa yanzu, an gano gawawwaki 42, kuma ana gudanar da aikin ceto a wurin da lamarin ya auku.

Wani jami'in gwamnatin jihar Niger seydou endak, ya alakanta faruwar hadarin jirgin da yawan mutanen da suka wuce kima da jirgin ya dauko.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China