Yanzu haka an shiga rana ta biyar da yin babbar muhawarar taron MDD karo na 68, a cikin jawabinsa, Nabil Fahmy ya nuna cewa, ba za a iya samar da wani sabon yanayi a gabas ta tsakiya ba, muddin ba a kawar da makaman nukiliya, da makaman kare-dangi ba, kuma rashin daukar wannan mataki a cewarsa na iya kawo nakasu ga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Bugu da kari Fahmy ya kalubalanci kasar Isra'ila, da ta shiga yarjejeniyar hana yaduwar marasa makaman nukiliya. Ya ce ya kamata kasashen duniya sun yi kokarin gudanar da taron kawar da makaman nukiliya a yankin gabas ta tsakiya, a karshen wannan shekara ko a farkon shekara mai zuwa, wanda a baya aka jinkirta gudanar da shi a shekara da ta gabata. (Amina)