in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu fafutuka dake arewacin kasar Mali sun sanar da dakatar da yarjejeniyar hana bude wuta ta Ouagadougou
2013-09-27 15:18:57 cri

Kabilar Tuareg dake arewacin kasar Mali ta ba da sanarwa a jiya Alhamis 26 ga wata da dare cewa, za su dakatar da yarjejeniyar hana bude wuta ta Ouagadougou da ta kulla tare da gwamnatin wucin gadi ta kasar.

A cikin wannan sanarwar, wadanda suka kulla yarjejeniyar ciki hadda kungiyar 'yantar da al'ummar Azawad ta NMLA ta nuna cewa, dalilin kin cika alkawari da kuma sabawa yarjejeniyar da gwamnatin Mali ta yi, hakan ya sa suka sanar da dakatar da wannan yarjejeniya. Ban da haka kuma, sun nemi sauran wadanda suka sa hannu kan yarjejeniyar da su kira wani taro cikin gaggawa a Ouagadougou domin duba yadda aka aiwatar da yarjejeniyar tun bayan da aka daddale ita. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China