Madam Maria Cristina Perceval, shugabar kwamitin sulhu ta wannan wata kuma zaunanniyar wakiliyar kasar Argentine a MDD ta karanta wannan sanarwa.
Dangane da batun arewacin kasar Mali, kwamitin sulhu ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka daddale a watan Yuni na bana a birnin Ouagadougou, hedkwatar kasar Burkina Faso, su kuma yi shawarwarin zaman lafiya da bangarori daban daban za su iya shiga da amincewa cikin lokacin da yarjejeniyar ta tsara, inda za su lalubo bakin zaren daidaita rikicin kasar ta hanyar siyasa cikin dogon lokaci, ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin dogon lokaci a sassa daban daban na Mali.
Har wa yau kuma, kwamitin sulhu ya yi kira ga Mali da ta gudanar da zaben 'yan majalisar kasar cikin hanzari, tare da tabbatar da 'yancin kai, da adalci ba tare da boye kome ba. Sa'an nan kwamitin sulhu ya jaddada muhimmancin yin shawarwari da samun sulhu a duk fadin kasar ta Mali. (Tasallah)