A wannan rana da dare, gidan telebijin na kasar ya bayar da labarin wannan umurnin shugaban kasar, amma ba a bayar da bayani game da yaushe ne za a kafa sabuwar gwamnatin kasar ba.
Oumar Tatam Ly da aka haife shi a birnin Paris da ke kasar Faransa, tsohon ma'aikacin banki ne, kuma ya taba zama mai ba da shawara ga babban bankin kasashen yammacin Afrika, kafin ya zama firaministan kasar. Sannan kuma, ya yi aiki a bankin duniya da sashen sakatariya na fadar shugaban kasar Mali, ban da wannan kuma, ya taba rike mukamin shugaban sashen babban bankin kasashen yammacin Afrika da ke kasar Mali.(Bako)