in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban kasar Mali ya yi rantsuwar kama aiki
2013-09-20 16:41:05 cri
A ranar Alhamis 19 ga wata, a birnin Bamako, sabon shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita ya yi rantsuwar kama aiki, a gaban shugabanni da wakilai daga kasashe sama da 20 da suka halarci wannan biki.

A safiyar ranar 19 ga wata, an yi gagarumin bikin a wani filin wasan motsa jiki, inda shugaban Faransa François Hollande, da shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, da sarkin Morocco Mohammed VI, da sauran shugabanni daga kasashen Nijer, Togo, Nijeriya, Ghana, Burkina Faso da sauransu suka halarta. A matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin, kana darektan kwamitin harkokin al'ummomin kasar Sin, Wang Zhengwei shi ma ya halarci wannan biki.

A wannan rana kuma, a fadar shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita ya gana da mista Wang, wanda ya isar da gaisuwar shugaba Xi ga mista Keita, inda ya furta cewa, ko a cikin yunkurin neman samun 'yancin al'umma, ko kuma kan sabon mataki na bunkasa tattalin arzikin kasa, jama'ar kasar Sin aminiya ce ta jama'ar kasar Mali.

A nasa bangare, shugaba Keita ya ce, a cikin wa'adin aikinsa, zai yi kokarin sa kaimi ga zurfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da fatan zumuncin dake tsakanin Mali da Sin zai kai wani sabon mataki. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China