in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ta cigaba da shirye shiryen bikin rantsar da sabon shugaban kasar Mali
2013-09-01 16:17:54 cri
Sabon shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita zai yi rantsuwar kama aiki a ranar hudu ga watan Satumba mai zuwa, bikin wanda a gabaninsa ake ta cigaba da gudanar da shirye shiryensa a cewar wata majiya mai tushe ta kwamitin dake kula da shirye shiryen bikin rantsar da sabon shugaban kasar. Mambobin wannan kwamiti da aka dorawa wannan nauyi ya kebe yinin ranar Asabar domin gudanar gwajin tsarin bikin yadda zai kasance. Sabon shugaban kasar Mali da aka zaba, Ibrahim Boubacar Keita, zai yi rantsar kama aiki a ranar hudu ga watan Satumba mai zuwa, wato makonni biyu bayan da babbar kotun tsarin mulkin kasar Mali ta bayar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasa, inda a yayin wannan biki sabon shugaban kasar Mali zai yi rantsuwar kama aiki a gaban kotun kolin kasar. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China