Bikin rantsarwar dai ya zo makonni biyu bayan sanar da samun nasarar babban zabe da aka jefa zagaye na biyu a ranar 11 ga watan jiya na Agusta kamar yadda kotun tsarin mulki na kasar ta shirya bisa doka mai lamba 37 na kundin tsarin mulkin.
A lokacin sanar da sakamakon zaben zagaye na karshe da aka yi a ranar 20 ga watan na Agusta Shugaba kotun tsarin mulkin kasar Amadi Tamba Camara ya sanar da sunan Ibrahim Boubacar Keita a matsayin zababben Shugaban kasa wanda ya samu kashi 77.62 a cikin 100 na kuri'un da aka jefa abinda yasa ya doke abokin hamayar sa Soumaila Cisse wanda ya samu kashi 22.38 a cikin 100 na kuri'un. (Fatimah Jibril)