in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban kasar Mali zai isa ranar yau Lahadi a kasar Nijar
2013-09-01 16:44:12 cri
Sabon shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita zai kai ziyarar aiki a kasar Nijar a ranar yau Lahadi, a cikin wani rangadin da ya fara tun yau da kwanaki uku a wasu kasashen dake cikin shiyyar yammacin Afrika, a cewar wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasar Nijar.

Wannan wata babbar dama ce ga Ibrahim Boubacar Keita, da aka zabe shi ranar 11 ga watan Augustan da ya gabata da kuma kafin yayi rantsuwar kama aiki a ranar hudu ga watan Satumba na ya zo kasar Nijar domin nuna yabo kan kasar Nijar da shugabanta bisa kokarin taimakawa warware rikicin kasar Mali, in ji wannan majiya.

Rangadin sabon shugaban kasar Mali na da manufar ba da goron gayyata ga shugaban kasar Nijar wajen halarta bikin rantsuwar kama aikinsa.

Kafin zaiyararsa a Nijar, zababben shugaban kasar Mali, ya je kasar Chadi da kasar Cote d'Ivoire, Burkina Faso da Togo da zummar gyayyata shugabannin wadannan kasashe.

Kasar Nijar dai ta tura sojoji 680 a cikin tawagar kasa da kasa ta taimakawa kasar Mali (MISMA) tun farko farkon barkewar rikicin kasar Mali a cikin watan Janairun da ya gabata domin fatattakar kungiyoyin ta'adanci dake arewacin kasar Mali, da kuma karbe 'yancin fadin kasar Mali daga hannun 'yan ta'ada.

Kasar Nijar na raba iyaka da kasar Mali bisa kilomita 400, kuma baya da haka al'ummomin kasashen biyu na magana da harsunan Tamajek, Songhai da Fulfulde da sauransu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China