Wannan cibiya wata kungiya ce ta kare hakkin dan adam a kasar Mali wanda daga cikin manufofin da ta sanya gaba shi ne na taimakawa wajen karfafa demokaradiyya a kasar Mali, ta yadda za'a janyo da kirkiro ayyukan da za su taimakawa wajen ba da azama ga 'yan kasar Mali wajen halarta ga kyautata zaman rayuwar al'umma, fadakar da horar da mutanen kasar kan 'yancin da nauyin dake bisa wuyansu ta hanyar watsa makaman shari'a da samar da taimakon shari'a ga 'yan kasa musamman ma ga talakawa.
Minista Malick Coulbaly, a cikin jawabinsa a yayin bikin, ya bayyana cewa a matsayinta na wata hukumar dake aikin bunkasa da kare hakkin dan adam, wadanda suka kirkiro wannan kungiya sun bayyana niyyarsu ta taimaka ma sake gina kasar Mali mai cike da 'yanci. (Maman Ada)