in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya kara tsawon lokacin aikin tawagar sa ido a Somaliya da Eritrea
2013-07-25 10:19:59 cri
A ranar Laraba 25 ga wata kwamitin sulhu na MDD ya kara tsawon lokacin aikin tawagar kwararru mai sa ido ta MDD kan tabbatar da hana shigar da makamai da kayayyakin soja a kasashen Somaliya da Eritrea.

A cikin kudurin, kwamitin ya tsai da shawarar kara tsawon lokacin aikin tawagar sa idon zuwa ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 2014, wacce har ila yau ita ce ke ayyukan binciken dukkan harkoki da suka hada da hada-hadar kudade da na teku, inda ta wadannan hanyoyi ne ake samun kudade da ake karya dokar ta hana shigowa da makamai.

Bisa wannan kuduri, kwamitin mai mambobi 15 ya tsai da shawarar cewa, takunkumi kan makamai a kasar Somaliya ba zai shafi samar da makamai da kayayyakin soja ko kuma ba da shawarwari, tallafi da horo ba, wadanda suka shafi bunkasa rundunonin tsaro na gwamnatin tarayyar kasar Somaliya domin samar da tsaro ga jama'ar kasar.

Kudurin har wa yau ya jaddada muhimmancin ganawa tsakanin tawagar sa idon da gwamnatin kasar Eritrea, kana ya nuna fatan cewa, gwamnatin za ta samar da dama ga tawagar ta shiga kasar ba tare da wani jinkiri ba. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China