in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birtaniya ta sake bude ofishin jakadancin kasar a Somaliya
2013-04-26 11:02:26 cri
A ranar 25 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Birtaniya William Jefferson Hague ya isa birnin Mogadishu hedkwatar kasar Somaliya, inda ya sanar da sake bude ofishin jakadancin kasar a kasar Somaliya. Wannan ofishin jakadanci shi ne ofishin jakadanci na kasashen kungiyar EU na farko da aka sake budewa a kasar Somaliya.

Hague ya halarci bikin daga tutar kasa da aka shirya a babban filin jiragen sama na Mogadishu. Bisa labarin da aka samu, an ce, an kafa ofishin jakadanci na wucin gadi na kasar Birtaniya a wannan babban filin jiragen sama, sabo da yanzu, ana yin gyare-gyare tsohon ofishin jakadancin kasar da ke Somaliya. Hague ya ce, bayan da ma'aikatan diplomasiyya na kasar suka janye daga birnin Mogadishu har tsawon shekaru 22, sake bude ofishin jakadancin Birtaniya a Somaliya zai zama abin sauyawar tarihi cikin dangantakar kasashen biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China