Manzon kungiyar AU mai kula da Somaliya ya yi kira da a hanzarta kawo karshen fadan da ake yi a birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin Somaliya, inda aka bayar da rahoton cewa fararen hula da dama sun rasa rayukansu.
A cikin wata sanarwa da aka bayar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, wakilin AU na musamman mai kula da Somaliya kana shugaban tawagar AU a Somaliya(AMISOM) Jakada Mahamat Saleh Annadif, ya ce duk da cewa, al'amura a kasar da ke kusurwar Afirka na ci gaba da inganta, har yanzu kasar tana fuskantar kalubale da dama,l amarin da ke bukatar kulawar gaggawa a bangaren shugabannin siyasa, addinai da kuma na al'ummar kasar.
Annadif ya fada a cikin sanarwar cewa, wajibi ne al'ummar Somaliya da kuma shugabanninta, su bayyana irin nasarorin tsaron da aka samu karkashin AMISON, dakarun tsaron Somaliya da kawayensu, a kokarin da ake na kara samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya ce wajibi ne kuma su yi amfani da wannan dama wajen kawo karshen rikicin siyasar da ya dagula shirin wanzar da lafiyar kasar ta Somaliya.
Wasu rahotanni da ba a tantance ba, sun bayyana cewa, fadan da ya barke a garin na Kismayo a ranar Jumma'a, ya sake tashi a ranar Asabar tsakanin mayakan da ke goyon bayan shugabannin 'yan tawaye a birnin. Kuma shugaban kasar ta Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud ya bayyana bacin ransa da wannan fadan.(Ibrahim)