Wannan taro da za'a shafe kwanaki uku ana yinsa, takensa shi ne "Hada gwiwa da nahiyar Afirka cikin kuzari". Inda shugabanni da wakilai daga kasashen Afirka 51, da shugabannin kungiyoyin duniya da dama suke halarta.
Shugaban kungiyar AU a wannan karo, kana firaministan Habasha, Hailemariam Desaleg A cikin jawabinsa wajen bude taron ya ce, albarkatun kwadago da kwarewar fasahohi, babban tushe ne na bunkasa nahiyar Afirka cikin dorewa. Tun da dadewa nahiyar ta kan fitar da muhimman kayayyakin amfani na masana'antu zuwa kasashen waje, yayin da ta kan shigar da kayayyakin masana'antu daga ketare. A nan gaba, dole ne ta kara kokarin bunkasa masana'antu na kanta.
A nasa jawabin shi ma, Babban Magatakardar MDD, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ko da yake kasashen Afirka sun sami babban ci gaba wajen gudanar da shirin bunkasuwa cikin sabon karni na MDD, sai dai kasashe da dama na ci gaba da fama da matsalar karancin abinci, kiwon lafiya, samun jiyya da sauransu, har ma wasu suna fama da tashe tashen hankula. Don a haka a kokarin daidaita wadannan matsaloli, dole ne a hada tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman samun bunkasuwa a gu daya.(Fatima)