A cikin shekaru 6 da suka gabata, saurin karuwar kudin da Sin ta samu wajen kera na'urorin ayyukan noma ya kai kimanin kashi 20 cikin 100 a kowace shekara, matsayin dake sahun gaba a duniya. Haka kuma, bisa kididdigar da aka fitar, an ce, yawan jiragen dankaro da Sin ta kera ya zarce miliyan 2 a shekarar 2012, yayin da yawan jiragen girbi da Sin ta kera ya kai sama da miliyan 1, wanda kuma ya nuna cewa, yawan irin wadannan na'urori biyu da Sin ta kera ya zarce na sauran kasashe ko jihohi nesa ba kusa ba.
Zhang Taolin ya ce, sakamakon shirin gaggauta kaurar da 'yan kwadago ke yi daga kauyuka zuwa birane, manoma za su kara bukatar na'urorin ayyukan noma masu yawa, matakin dake nuna shiga wani kyakkyawan yanayi a fannin kera na'urorin ayyukan na noma.(Bako)