in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin ya gana da firaministan kasar Namibia
2012-05-18 10:49:10 cri

A ranar 17 ga wannan wata a Windhoek, babban birnin kasar Namibia, firaministan kasar Nahas Angula ya gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma mataimakin shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Gang dake ziyara a kasar Namibia.

Angula ya bayyana cewa, kasar Namibia ta nuna godiya ga kasar Sin dake nuna goyon baya ga kasarsa cikin dogon lokaci, kana Namibia na fatan kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da ciniki da kuma fasahohi domin inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi.

Wang Gang ya isar da gaisuwar firaministan kasar Sin Wen Jiabao ga Angula, kana ya ce, bayan da aka kulla dangantaka a tsakanin kasashen biyu duk da cewa ana samun sauye sauye a duniya, amma har yanzu kyakkyawar dangantakarsu tana nan yadda ya kamata. A wasu shekaru da suka gabata, shugabannin kasashen biyu sun yi ganawa sau da dama, da samun fahimtar juna a fannin siyasa, da samun nasara kan hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da yin mu'amala da juna a fannin al'adu, da kuma yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa da yankuna.

A wannan rana, Wang Gang ya yi shawarwari tare da shugabar jam'iyyar SWAPO ta kasar Namibia madam Ithana. Inda Wang Gang ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dora muhimmanci kan raya danganatkar dake tsakaninta da jam'iyyar SWAPO ta kasar Namibia, kana tana son yin kokari tare da jam'iyyar SWAPO wajen sa kaimi ga yin ganawa a tsakanin shugabannin kasashen biyu, da yin mu'amala a fannin harkokin siyasa, da inganta hadin gwiwar kasashen biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin jama'arsu, ta yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin jam'iyyun biyu zuwa wani sabon matsayi.

Ithana ta nanu fatan jam'iyyun biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban don sa kaimi ga ci gaban dangantakar kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China