"Yarjejeniyoyin da ake shirin sa hannu kansu albarkacin wannan zaman taro suna nuna nacewa da muhimmancin wannan dangantaka da muke neman baiwa wani babban matsayi." in ji ministan harkokin wajen kasar Congo(Brazzaville) mista Basile Ikouebe a yayin bikin bude wannan taro.
Shi dai wannan zaman taro na kungiyar hadin gwiwa ta biyu mafi girma ya hada da kwararru daga kasashen biyu, wanda za'a kammala ayyukan taron a ranar Jumma'a nada manufar kafa harsashin bunkasuwar yarjejeniyoyin da aka sa hannu a shekarar 2007 tsakanin kasashen biyu, musammun ma kan batutuwan kamun kifi, kiyaye tsaron sararin sama, kasuwanci da ilimin kimiyya da fasaha.
Haka kuma taron zai cimma wasu sabbabin yarjejeniyoyin da suka shafi wasu fannoni daban daban kamar batun sufuri ta hanyar ruwa da maganar dazuzzuka.
"Wannan kungiyar hadin gwiwa, wata muhimmiyar hanya ce dake ba mu damar cimma burinmu a fuskar tattalin arziki da zaman al'umma kamar yadda shugabanninmu suka tsai da a shekarar 2007." a cewar mista Utoni Nujoma, shugaban tawagar kasar Namibiya kuma dake rike da matsayin ministan harkokin wajen kasar.
"Haka kuma makasudin kafa wannan dangantaka tsakanin kasashen biyu shi ne na samar da yanayi mai kyau wajen bunkasa tattalin arziki mai dorewa domin kyautatuwar zaman rayuwar al'ummar kasashen biyu." ya kara da cewa.
Bisa jadawalin ayyukan wannan zaman taro, bangarorin biyu za su mai da hankali kan wani tsarin sake gina wata makarantar koyar da aikin hannu da fasaha a birnin Loudima dake cikin jihar Bouenza na Congo(Brazzaville).
Tun samun 'yancin kai a shekarar 1990, kasar Namibiya take tafiyar da huldarta da kasar Congo(Brazzaville) cikin zumunci da zaman lafiya. Haka kasar na da arziki kamar kasar Congo (Brazzaville) da Allah ya hore mata mai yawan gaske kuma iri daban daban dake ba kasashen wata babbar damar cin gajiyar dangantakarsu cikin moriyar juna.(Maman Ada)