in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai kyakkyawar makoma ta fuskar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Namibia
2011-05-22 17:02:23 cri
Shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo, wanda ke yin ziyara a kasar Namibia ya bayyana a ranar 21 ga wata cewa, kasashen Sin da Namibia na bukatar juna ta fuskar tattalin arziki, kuma an kafa tushe mai kyau ga hadin gwiwarsu, saboda haka akwai kyakkyawar makoma wajen karfafa hadin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

A yayin da yake ganawa da shugaba Hifikepunye Pohamba na kasar Namibia a wannan rana a birnin Windhoek, Wu ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan kara kokari tare da Namibia don ciyar da dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci tsakanin kasashen biyu gaba. Kazalika Wu ya ba da shawarwari kan bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

A nasa bangaren kuma, Pohamba ya bayyana cewa, kasar Namibia na fatan kara yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da Sin cikin dogon lokaci a dukkan fannoni.

Bayan haka kuma, shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa, kasashen biyu za su ci gaba da karfafa hadin kai, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa bisa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma kara wasu abubuwan da ke da nasaba da sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu.

A wannan rana kuma, Wu Bangguo da Pohamba sun halarci bikin bude taron dandalin shugabannin matasa na Sin da kasashen Afrika da aka shirya a birnin Windhoek, inda shugabannin biyu suka yi fatan cewa, matasan Sin da na kasashen Afrika za su kara inganta dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.

Wakilai matasa fiye da 200 da suka fito daga kasar Sin da kasashen Afrika guda 17 sun halarci dandalin.

A ranar 22 ga wata, Wu Bangguo ya isa Luanda, babban birnin kasar Angola, don yin ziyarar aiki a kasar.  A lokacin ziyararsa, Wu zai yi musayar ra'ayoyi sosai tare da wasu shugabannin kasar Angola, ciki har da shugaban kasar, da shugaban majalisar dokoki, da sauransu. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China