in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin shugaban kasar Namibiya da Liu Yandong
2011-12-01 15:33:16 cri

Ranar Laraba 30 ga watan Nuwanba a Windhoek babban birnin kasar Namibiya, shugaban kasar Hifikepunye Pohamba ya gana da Liu Yandong mambar majalisar gudanarwa ta kasar Sin.

Yayin ganawar, Liu Yandong ta ce, kasar Sin tana fatan kara yin hadin kai tare da kasar Namibya domin zurfafa zumunci da habaka hadin kai tsakaninsu a fanonin daban-daban.

Liu Yandong ta yi bayyani cewa, yin musayar ra'ayi a fannin al'adu zai taka muhimiyar rawa wajen habaka hadin kai tsakaninsu a dukkan fannoni.

A nasa jawabin Shugaba Hifikepunye Pohamba ya yaba ma ci gaban da aka samu tsakanin kasashen biyu tare da nuna godiya ga taimakon da Sin take baiwa kasar a fannin kayayyaki da fasahohi cikin dogon lokaci. Ya nuna cewa, kasar Namibya tana fatan zurfafa hadin kai tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, makamashi, al'adu, ba da ilmi, kimiya da sauransu.

A wannan rana har ila yau, Liu Yandong ta sanar da shawara da gwamnatin kasar Sin ta yanke wajen kafa wani asusu a kungiyar UNESCO ta MDD daga shekarar 2012 zuwa ta 2015 domin taimakawa kasashen Afrika wajen bunkasa ayyukan ba da ilmi.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China