A yayin shawarwarin, Wu ya ba da shawarwari guda hudu da zummar zurfafa hakikanin hadin gwiwa da inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu. Da farko, ci gaba da yin mu'amala tsakanin manyan jami'ai na kasashen biyu da tabbatar da hanyar da za su bi wajen bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Na biyu, zurfafa hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu, musamman ma a fannin zuba jari. Na uku, karfafa mu'amalar al'adu. Na hudu, musayar ra'ayoyi kan harkokin duniya da na kasashen Afirka cikin lokaci domin samun hadin gwiwar juna, tare da kiyaye moriyar kasashen biyu da ta sauran kasashe masu tasowa.
A yayin da ake tabo maganar yin mu'amala tsakanin majalisun biyu, Wu ya bayyana fatansa na ganin cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar dokokin Namibia za su kara yin musayar ra'ayoyi da samun fasahohi daga juna a fannonin kula da harkokin kasa, bunkasa tattalin arziki da dai sauransu.
Theo-Ben Gurirab ya nanata manufar da Namibia take tsaye a kai ta daukar kasar Sin daya tak. Kuma Namibia ta nuna goyon baya ga Sin wajen ganin dinkuwar duk kasar baki daya.(Fatima)