in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Namibiya ya gana da mamban ofishin siyasa na babban kwamitin JKS
2012-05-19 17:06:34 cri
A ranar 18 ga wannan wata a birnin Windhoek, shugaban kasar Namibiya, kana shugaban jam'iyyar SWAPO, Hifikepunye Pohamba ya gana da mamban ofishin siyasa na babban kwamitin na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin, Wang Gang, wanda yake ziyara a wannan kasa.

Shugaba Pohamba ya bayyana cewa, kasashen Namibiya da Sin suna da zumunci na dogon lokaci. Namibiya na fatan kara hadin kai da Sin a fannoni daban daban cikin dogon lokaci kuma bisa manyan tsare-tsare.

A nasa bangare, da farko mista Wang ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Hu Jintao. Kuma ya furta cewa, dangantaka tsakanin kasashen biyu irinta girmamawa juna ce a fannin siyasa, da samun moriyar juna a fannin tattalin arziki, da yin mu'amala a fannin al'adu, za ta zama abin koyi ga kasashe masu tasowa kan yadda za su yi hadin gwiwa a tsakaninsu. Sin da Namibiya abokan arziki ne a ko da yaushe. A sabili da haka, Wang ya kara da cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan karfafa da bunkasa zumunci dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Sin na fatan yin kokari tare da Namibiya, ta fannin kara amincewa da juna a bangaren siyasa, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da zurfafa mu'amala a fannin al'adu, ta yadda za su sa kaimi ga bunkasa dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Namibiya zuwa wani sabon mataki.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China