in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar 'yan wasan kwallon kafan kasar Namibia za su iso Najeriya a ranar Alhamis
2012-05-30 14:30:18 cri
A ranar Talata ne hukumar kwallon kafa ta Najeriya(NFA) ta sanar da cewa, a ranar Alhamis ne ake saran isowar tawagar kwallon kafan kasar Namibia mai mutum 25 da aka fi sani da suna Brave Warrriors, za ta iso Lagos da yamma ta jirgin saman Lufthansa daga birnin Frankfurt na kasar Jamus.

Hukumar ta NFA ta ce, tawagar ta kunshi jami'an horaswa, ma'aikatan yau da kullum kana jami'an NFA guda 3 su ma za su iso Lagos a wannan rana ta jirgin saman kasar Afirka ta kudu, wanda zai taso daga birnin Johannesburg.

'Yan wasan na Brave Warriors da suke samun horo a kasar Jamus, sun yi kunnen doki da kasar Mozambique a wasan sada zumuncin da suka yi a ranar Lahadin da ta gabata a kasar Jamus.

A ranar Lahadi ne za a fara wasan share fage na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara 2014 a Afirka a filin wasan na U.J. Esuene da ke Calabar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China