An kulla wannan yarjejeniyar ne bayan da ministocin Namibia da wasu jami'ai na ma'aikatun kasar suka yi tattaunawar da mambar majalisar gudanarwar kasar Sin Madam Liu Yandong yayin da take ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar ta Namibia tun daga ranar Talatar da ta gabata.
Albert Kawana, ministan harkokin shugaban kasar Namibia kuma darektan janar na rikon kwarya a hukumar tsara shirye-shirye ta kasar, da jakadan kasar Sin a Namibia Wei Ruixing su ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.
Kazalika kasashen biyu sun yi musayar takarda, wadda gwamnatin Sin za ta samar da wasu kayayyakin aiki na ofis da kayayyakin da suke samar da wutar lantarki ta hasken rana ga kasar Namibia.
Yayin da suke tattaunawar, Madam Lui ta bayyana irin yadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke kara karfafa a ko da yaushe.
Ta kara da cewa, kawo yanzu daga cikin muhimman abubuwan da aka kulla sun hada da aikin noma da albarkar ma'adanan kasa, kazalika da an cimma maganar musayar ilimi da al'adu.
A nata bagaren mataimakin firaministan Namibia Marco Hausiku ya bukaci hadin kai da kasar ta Sin a fannin nune-nune na al'adu. (SALAMATU)