Jaridar ta bayyana cewa, bayanin hakan ya fito ne daga bakin Al-Muiz Farouq, mai daidaita bayanai a bangaren siyasa da tsaro tsakanin kasashen biyu, wanda ya ce kwamitin na kungiyar AU ta riga ta fara aiki tare da tabbatar da wurare uku da za ta duba gabannin tsai da shati da ba mallakin kowa ba kamar yadda taswirar kungiyar zata fitar.
Al-Muiz yace, ana sa ran kwamitin zai kammala aikinsa a tsakiyar wannan wata da muke ciki na Agusta, yana mai bayanin cewa, tuni wata tawagar da za ta kula da wannan aikin ta riga ta isa garin Kadogli a kudancin Kordofan kuma ta riga har ta gana da ma'aikatan duba yuwuwar hakan dake wakiltar kasashen biyu.(Fatimah Jibril)