A cewar wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Khartoum ya bayar, wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafinta, ana saran yayin tattaunawar da za su yi bangarorin biyu za su yi musayar ra'ayoyi game da dangantakar da ke tsakaninsu, da kuma yanayin da ake ciki tsakanin Sudan da Sudan ta kudu.
Bugu da kari sanarwar ta ce, Zhong ya tattaunawa da ministan harkokin wajen kasar Sudan Ali Karti, ganawar da ta samu halartar jakadan Sin da ke Khartoum Luo Xiaoguang, darekta mai kula da harkokin kasar Sin a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan.(Ibrahim)