A ranar Juma'a 16 ga wata, wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ya amince da yin wata ganawa, ranar 20 ga watan Agusta a birnin Khartoum, in ji kamfanin dillancin labaran kasar Sudan SUNA.
Mai Magana da yawun sojin kasar Sudan Al-Sawarmy Khalid Saad, ya bayyana cewa, ministan tsaro na kasar Sudan Abdul-Rahim Mohammed Hussein da takwaransa na Sudan ta Kudu Kuol Manyang Juuk sun zanta ta wayar tarho ranar Juma'a, inda a lokacin ne suka amince da kiran wata ganawa na kwamitin hadin gwiwa ranar 20 ga watan Agusta.
Ya kara da cewa, bangarorin biyu sun kuma amince kan yadda za'a aiwatar da yarjeniyoyi da sake farfado da hanyoyin tabbatar da aiwatar da batutuwa da suka shafi tsaro.
A ranar 27 ga watan Satumba na 2012, kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun rattaba hannu kan yarjejeniya a kan wasu batutuwa daban daban yayin wata ganawar shugabannin kasashe a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.(Lami Ali)