A cikin wasikar da aka sanya kwafinta a shafin sada zumunta na facebook, Netanyahu ya bayyana cewa, ba zai amince da sharadin da Palesdinu ta sanya don gane da bude shawarwarin shimfida zaman lafiya ba, wato Isra'ila ta dakatar da gina matsugunan Yahudawa, ya ce za a saki wadannan Palesdinawa ne mataki mataki yayin da ake gudanar da shawarwarin. Netanyahu ya ce, wannan ne kuduri mafi wuya da aka tsaida, kuma ko da yake a matsayinsa yana iya tsaida kudurin da ya saba da ra'ayin jama'arsa a wani lokaci domin cimma manyan bukatun kasar.
Ban da wannan kuma, Netanyahu ya bayyana cewa, sake bude shawarwarin shimfida zaman lafiya yana da muhimmanci sosai ga Isra'ila, domin hakan zai kawo karshen rikicin dake tsakaninta da Palesdinu, kana zai bada kyakkyawar dama ga kasar Isra'ila wajen zurfafa matsayinta a duniya. (Zainab)