A wani cigaban kuma sakataren wajen kasar ta Amurka John Kerry, ya bayyana sunan tsohon jakadan Amurka a Isra'ila Martin Indyk, a matsayin wakilin musamman na Amurka da zai shiga tsakani yayin tattaunawar da bangarorin biyu zasu gudanar.
Ana dai sa ran tattaunawar da wakilan bangarorin biyu suka fara a ranar Litinin, zata share fagen cimma cikakkun yarjejeniyoyi nan da watanni 9 masu zuwa.
A ranar Lahadin da ta gabata ma dai mahukuntan Isra'ila sun amince da sakin firsinoni Falasdinawa 104 da Isra'ilan ke tsare da su, a matsayin cika daya daga sharuddan da Falasdinu ta gindaya gabannin komawarta teburin shawara.
A yayin zaman tattaunawar ranekun Litinin da Talata, manyan jami'an hukumomin bangarorin biyu, ciki hadda ministan shari'a, kuma babban jami'in shirin tattaunawar daga tsagin Isra'ila Tzipi Livni, da kuma wakilin fadar Firaministan kasar Yitzhak Molcho, na cikin wadanda suka samu halarta. Yayin da daga bangaren al'ummar Falasdinawa kuma, babban mai shiga tsakani Saeb Erekat, da jigo a jam'iyyar Abbas Fatah Mohammad Shtayyeh suka halarci tattaunawar. (Saminu)