in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Israila da Falasdinu.
2013-08-01 10:31:54 cri
Kakakin ma'aikatar kasashen wajen kasar Sin a jiya Laraba 31 ga watan Yuli ya sanar da maraban da kasar ta yi game da farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin kasar Israila da yankin Falasdinu.

Masu shiga tsakani na wannan tattaunawa sun gana da juna a birnin Washington, fadar gwanmnatin kasar Amurka a ranar Litinin din da ta gabata domin share fagen farfado da tattaunawar zaman lafiya da aka dakatar a watan Octoban shekara ta 2010 sakamakon fadada matsugunan yahudawa da Israila ta yi a yankin Falasdinu.

A lokacin ganawar sa da manema labarai a ranar Talata, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce, masu shiga tsakani a tattaunawar Israila da Falasdinu sun amince su sake ganawa da juna nan da makonni biyu ko a yankin Israila ko kuma a yankin Falasdinu.

Bangarorin biyu sun kuma amince za su yi zaman tattaunawa a cikin a kalla watanni 9 domin samar da mafita na kawo karshen takaddamar dake tsakanin su na shekaru fiye da 60.

A cikin wata sanarwa da aka bayar a rubuce, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Hong Lei ya ce kasar tana goyon bayan bangarorin biyu wajen ayyukan shawo kan matsalolin su da kuma aiki tare domin ingiza samar da cigaba mai armashi a lokacin tattaunawar.

Kasar Sin in ji shi a shirye take a ko da yaushe wajen inganta tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, yana mai bayanin cewa kasar za ta yi aiki da sauran kasashen duniya domin bada gudumawar ta ga samar da zaman lafiya tsakanin Israila da Falasdinu tare da samar da tsaro da daidaito a yankin gabas ta tsakiya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China