in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Barcelona na fatan amfani da kwallon kafa wajen bunkasa zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila
2013-08-16 15:35:18 cri

Shugaban kasar Isra'ila Peres ya bayyana cewa, yaran kasarsa ta Isra'ila da na Palesdinu suna da buri biyu. Na farko shi ne, samun nasarar kungiyar a dukkanin wasanninta da take bugawa a filinta na Camp Nou. Na biyu kuwa shi ne samun zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Shugaba Peres ya ce, wasanni, musamman ma na kwallon kafa zasu kawar da bambance-bambance, da kawo kyakkyawan fata ga yara a dukkanin fadin duniya. Burin da ya dace da wannan ziyara ta kungiyar ta Barcelona. Har ila yau jama'ar Palesdinu da Isra'ila za su iya yin amfani da fasahohin wasan kwallon kafa na kungiyar, da ya hada da mika kwallo tsakanin 'yan wasa bi-da-bi, don tabbatar da burin da aka sanya gaba.

A daren ranar 4 ga wata bayan kammala wannan ziyara, membobin kulaf din na Barcelona sun tashi daga kasar Isra'ila zuwa kasar Thailand, don gudanar da wasa da aka shirya tsakaninsu da wani kulaf din kasar na Thailand. Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a yi amfani da dukkan kudin da aka samu daga ziyarar kungiyar Barcelona a Palesdinu da Isra'ila a wannan karo ne wajen sa kaimi, ga bukatar wanzar da zaman lafiya a tsakanin sassan biyu. (Zainab)


1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China