in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulaf din kasar Juventus na shirin daukar kofin gasar Serie A a karo na gaba, a cewar daya daga 'yan gaban kulaf din
2013-07-19 16:57:00 cri
Yayin da ake batun yiwuwar sauyin sheka ga dan wasan tsakiyar AC Milan, shi kuwa na kulaf din Juventus Simone Pepe cewa yayi kulaf din su, ya fara shirin daukar kofin gasar zakarun kasar ta Italiya wato Serie A karo na Uku a jere, a yayin kakar wasa dake tafe.

Yanzu haka dai kulaf din na Juventus ya karfafa kansa da 'yan wasa irinsu Carlos Tevez da kuma Fernando Llorente, wadanda zasu fara murza leda a kulaf din nan da dan lokaci, matakin da acewar Pepe zai basu damar sake kafa tarihi a gasar ta Serie A, dama ragowar wasanni da kulaf din zai buga a nahiyar Turai baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China