Frank wanda shi ma ya taba bugawa kwallo din na FC Barcelona wasa a baya, ya bayyana a shafin yanar gizo na kulaf din na Ajax cewa, Bojan Krkic ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan wasa, wanda ya kware wajen cin kwallo, yana kuma iya tallafawa sauran 'yan wasa. Don haka, ya yi magana da shi, don lallashinsa ya amince zuwa kungiyar ta Ajax, inda za a sanya shi buga bangaren dama a gaba, ko da yake yana iya buga tsakiya ko kuma bangaren hagu.
Krkic dake da shekaru 22 a duniya, ya buga kwallo a kulaflikan AS Roma da AC Milan a kakar wasanni 2 da suka gabata. Yayin da yake AS Roma, ya buga wasanni 33 a gasar Serie A ta kasar Italiya, inda ya ciwa kulaf din kwallaye 7. Sa'an nan, a AC Milan, ya samu nasarar jefa kwallo 3 a wasanni 19 da ya buga.
Krkic ya fara samun horo ne a makarantar horar da matasan 'yan wasa ta FC Barcelona, sa'an nan ya fara buga gasar wasanni a shekarar 2007 yana dan shekaru 17 a duniya. Wa'adin kwangilarsa tare da Barcelona zata cika a shekarar 2015. Ko da yake kulaf din Ajax zai iya tsawaita wa'adin aronsa da karin kakar wasa guda.