in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Barcelona na fatan amfani da kwallon kafa wajen bunkasa zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila
2013-08-16 15:35:18 cri


Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Spaniya, ta kammala ziyararta a yankunan Palesdinu da Isra'ila a ranar Lahadi 4 ga wannan wata na Agusta da muke ciki, a yunkurinta na amfani da kwallon kafa wajen habaka zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakankanin matasan bangarorin biyu.

Bayan ziyararta a birnin Bethlehem dake yammacin gabar kogin Jordan a ranar 3 ga wata, kungiyar ta Barcelona ta kuma kai ziyara a birnin Kudus, da Tel Aviv a ranar 4 ga wata. A wannan rana, dukkan membobin kungiyar da mai horas da 'yan wasanta sun ziyarci mashahurin wurin Ibadan dake bangon yamma a birnin Kudus. Yayin wannan ziyara, ministan kula da harkokin yawon shakatawa na kasar Isra'ila Uzi Landau, ya mikawa shugaban kulaf din Sandro Rosell, takardar zumunta ta Isra'ila, wadda ke dauke da fatan ziyarar kungiyar, za ta inganta sha'anin yawon shakatawa a kasar ta Isra'ila.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China