in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Barcelona na fatan amfani da kwallon kafa wajen bunkasa zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila
2013-08-16 15:35:18 cri

Kungiyar Barcelona tana daya daga cikin manyan kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashen waje, da suka fi samun karbuwa a Palesdinu da Isra'ila, take kuma da tarin yara da matasa masu goya mata baya. Wannan dai darasin horaswa da kungiyar Barcelona ta bayar, ya sanya farin ciki kwarai da gaske a zukatan yaran, kasancewar hakan ya basu damar ganin manyan 'yan wasan da suke kauna, wadanda kuma suke burin koyon fasahohi taka leda daga wurinsu ido da ido. Ban da yaran da suka samu horon akwai kuma yara da dama da suka kalli wannan wasa, suma farin cikinsu bai gaza na yaran da suka samun horon ba. Ga wadannan yara, ziyarar kungiyar Barcelona ta cika musu burinsu na tsawon lokaci.

Makasudin ziyarar kungiyar Barcelona a wannan karo shi ne, sa kaimi ga samun zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila ta hanyar wasan kwallon kafa. Kamar dai yadda a halin da ake ciki, aka sake bude shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin sassan biyu, tare da burinda gwamnatocin bangarorin biyu keda shi na kyautata dangantakarsu, don haka ziyarar kungiyar ta Barcelona a wannan lokaci ta yi daidai da burin da aka sanya gaba.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China